Print Friendly, PDF & Email

Ƙungiyoyin ‘Yan Bindiga Masu Kawo Rashin Kwanciyar Hankalin Arewa Maso Yammacin Najeriya

ƙarin tasowan hare-haren da ƙungiyoyin ‘yan bindiga ke kaiwa al'umomi a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, har da sace-sacen jama'a na yaran makaranta, cin zarafin takaitaccen kasancewar ɓangaren tsaro a yankin.


Criminal bandit gang in Birnin Magaji

Ƙungiyan ‘yan bindiga a cikin Birnin Magaji, Jihar Zamfara. (Hoto daga Dr. Murtala Rufa’i)

Waɗanda aka fi sani a kafafen yada labarai na ƙasa da sunan “’yan bindiga”, ƙananan ƙungiyoyin ‘yan bindiga na sun kasance suna karuwa da yin barazana ga yankin Arewa maso yammacin Najeriya, kwacen shanu, fashi, da karbar kuɗin fansa daga gonakin ƙarkara da ƙauyuka. Waɗannan ƙungiyoyin ba sa jinkirin yin amfani da tashin hankali, gami da kisan kai, don tsoratar da mazaunan ƙauyukan don sa su yi biyayya. Tun daga shekarar 2020, an ba da rahoton cewa waɗannan ƙungiyoyin ‘yan bindigan suna da hannu a cikin tashe-tashen hankula sama da 350 da ke da alaƙa da asarar rayuka sama da 1,500. Wannan yana wakiltar karuwar hare-hare kusa da kashi 45 cikin 100 da kuma karuwar mace-mace kusa da kashi 65 cikin 100 idan aka kwatanta da lokacin 2018 zuwa 2019. Ba a ruwaito a cikin labaraiYawancin ƙananan hare-hare da sace-sace mutane ba a ba da rahoto ba.

Sun samu ƙarfafawa da kuma ƙara tsari azaman ƙwararrun masana’antar aikata laifuka, waɗannan ƙungiyoyin ‘yan bindigan sun samu shigan kanun labaran duniya da wasu jerin hare-hare na sacen mutane  a makarantun kwana a jihar Kaduna, Katsina, Niger, da Zamfarasuka. Wanda aka azabtar da su, a galibi ana gaskuwa da su don karbar babbar kuɗin fansa, sau da yawa suna sa iyalai da abin ya shafe su, su yi fatara. Don ƙarin rashin tsaro ga waɗannan hare-haren, ɗaruruwan makarantu sun rufe kuma sama da yara miliyan ɗaya a yankin ba sa zuwa karatu.

Waɗannan al’amura da wasu hare-hare sun tunzura hukumomin Najeriya zuwa sanya dokar atsewar sadarwar wayar hannu a yankin da kuma takura zirga-zirga da manyan tarurruka. A kwanan nan, wata kotun tarayya ta yanke hukunci bisa ga umarnin Daraktan Ƙararrakin Jama’a cewa ƙungiyoyin ‘yan bindiga nan na Arewa maso Yamma sun zama “’yan ta’adda,” wannan ya bayar da damar sassauta ka’idojin aikin soja. Duk da haka, martanin tsaro maras banbanci zai iya ƙara rashin zaman lafiya.

Cibiyar Nazarin Dabarun Afirka ta zanta da masana ‘yan Najeriya biyu game da tabarbarewar tsaro a yankin Arewa maso Yamma. Kunle Adebajo ɗan jarida ne wanda ya ba da labari sosai a kan rikicin ‘yan bindiga, kuma Dr. Murtala Rufa’i malami ne a Sashen Tarihi na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.

 *     *     *

Map - North West Nigeria

Me ya sa rashin tsaro da bala’in aikin agaji da ke addabar Jihohin Arewa maso Yamma ya kara ta’azzara kwanan nan?

ADEBAJO: Hakika, lamarin Arewa maso Yamma yana kara ta’azzara. An samu karuwar tashe-tashen hankula, mace-mace, da sace-sacen mutane kamar yadda [Majalisar Hulda da Kasashen Waje’] ta rubuta Lura da Tsaro Najeriya (Nigeria Security Tracker (NST)). An riga da ninki garkuwa da mutane a 2021 a Arewa maso Yamma idan aka kwatanta da 2020. Wannan ya ci gabar da tabarbarewar halin da ake ciki a shekaru da yawa da suka gabata wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 1,000 a kowane shekara. Yana yiwuwa cewan wanan ƙanƙantan ƙidaya ne. Yanzu haka akwai sama da mutane 450,000 da suka rasa matsugunansu (IDPs) a bisa lafazin Kungiyar Hijira ta Duniya—wasu majiyoyin sun nuna cewa adadin ma ya fi yawa.

A baya dai an fi yawan kai hare-hare a yankunan karkara, amma a yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da abkawa daga maboyarsu a cikin mafi nisan al’ummomi. Wannan na faruwa saboda yawancin wuraren nan ne aka yi ta kai masu hare-hare akai-akai kuma an ƙara talautar da su. Don haka haka ƙungiyoyin ‘yan bindiga sun na maida hankalinsu ga al’ummomin birane domin samun karin kuɗi, da kuma satar shanuka da yawa, kuma don karbar makudan kuɗaɗen fansa.  Yanzu kun ga cewa ƙungiyoyin ‘yan bindigan sun fi kai hari akai-akai ga hedikwatar kananan hukumomi da manyan al’ummomin da ke kusa da manyan titunan tarayya—-musamman tunda sun sami ma’aikata da makamai na tunkarar manyan hari. A bana dai ‘yan bindiga sun kai hari a sansanonin sojoji da ofisoshin ‘yan sanda a Zamfara da Sakkwato, lamarin da ya ba su damar samun karin makamai.A bana dai ‘yan bindiga sun kai hari a sansanonin sojoji da ofisoshin ‘yan sanda a Zamfara da Sakkwato, lamarin da ya ba su damar samun karin makamai.

Wani babban al’amari kuma shi ne rashin isassun ‘yan sanda da gine-ginen sojoji a yankunan da abin ya shafa Al’ummomin da ke da tawagar ‘Yan Sanda Masu Yawo (MOPOL) sun zama kamar garuruwan sansanin tsaro na Arewa maso Gabas kuma suna da aminci sosai fiye da sauran.
mafi aminci. Don haka, mutanen da ba su da irin wannan kasancewar ‘yan sanda suna ƙaura zuwa waɗannan wurare masu amincin, ƙaura na dindindin ko kuma kawai na cikin dare lokacin da hare-hare suke fin yawa. An kuma gano cewa kasancewar gungun ‘yan banga ko ‘yan tsaro da makamai na al’umma don dakile ‘yan fashi. Duk da haka, wannan yana iya zama takobi ne mai kaifi biyu  domin ‘yan banga na iya kai harin ramuwar gayya kan  al’ummar makwabcinsu da ke  makiyaya dabbobi. A in the midst of haka ana samun wuce gona da iri da kashe-kashen da ba bisa ka’ida ba.

MOPOL ta Najeriya

‘Yan sanda a Jihar Kaduna. (Hoto: Allan Leonard)

Rundunar ‘Yan Sanda Masu Yawo wadda aka fi sani su da MOPOL, ita ce  sashin dakarun sa-kai na ‘Yan Sandan Nijeriya da a asali an kafa tun a shekarar 1961 matsayin rundunar yaki da tarzoma. Amma an faɗaɗa ayyukanta zuwa wasu yankuna har da murkushe manyan tashin hankalin makami. Ana tura jami’in su zuwa faɗin kasan don kare kadarorin kasa da muhimman mutane, da kuma kawon zamman lafiya a wuraren da ba su da kwanciyar hankali, da kuma yaki da masu tayar da hankali wadanda ba gwamnati ba ne. Ana imanin cewan sun fi ‘yan sanda na yau da kullun aiki, ma’aikatan suna aiki tuƙuru a  matsayin daya daga cikin masu yaƙi da ta’addanci a Arewa maso Gabas kuma suna da sanannen kasancewa a Arewa maso Yamma inda suke kare al’umma daga hanun ‘yan bindiga.

RUFA’I: A shekaru ana tabarbarewar tsaro a yankin Arewa maso Yamma domin gwamnatin tarayya da na jihohi ba su yi la’akari da yadda matsalar ‘yan bindigan ke ta’azzara ba, kamar yadda suka saba , su cika yin rashin la’akari da tsananin tabarbarewar tsaron (a wasu lokaci suna hana kungiyoyin agaji shiga da hana kafa sansanonin ‘yan gudun hijira). Gwamnati ba ta saka hannun jari don fahimtar yanayin yankin da yadda kungiyoyin ‘yan bindiga ke aiki a cikinsa ba, don haka, ba su taɓa samar da daidaitattun ko ingantattun tsare-tsare don magance karuwar sace-sacen mutane da hare-haren da waɗannan ƙungiyoyin ke gudanarwa ba.

A cikin shekarar da ta gabata, matakan COVID-ciki har da rufe iyakokin kasa da kasa da Nijar, ƙuntatawan kasuwa, da dokar hana fita – sun haifar da wahalhalu da yawa ga mutane a yankin Arewa maso Yamma. Talauci da rashin aikin yi sun karu, kuma mun lissafta su a binciken al’ummomin karkara. Da farko, cinikin tsakanin iyakoki ya tsaya cik, amma sai dagabaya harkokin ciniki na yau da kullun ya koma dawowa. Amma, cin hanci da rashawa ya karu tun da cewa a hukumance, an dakatar da waɗannan ayyukan. Kungiyoyin ’yan bindiga sun yi amfani da wannan al’amari ta hanyar samar da kayan abinci ga wasu al’ummomin da ke fama da wahala sannan suka ɗauki matasa maza da masu ba da bayanin sirri. Wannan tsari ne da suka bi a lokacin da suka gabata—cin zarafin talakawa a lokacin da gwamnati ta yi  almundahana ko kuma babu gwammnati.

Akwai ƙauyuka da yawa waɗanda ke zama a matsayin al’umman masaukan ga wasu ƙungiyoyin ‘yan bindigan. Kungiyoyin sun fake a cikin dazuzzukan da ke kusa da kauyukan, kuma suna barin su ci gaba da rayuwa kamar yadda aka saba idan dain waɗannan kauyukan sun ba da haraji da kuma ba su ma’aikata. Hakazalika, ‘yan bindigan suna kare waɗannan kauyuka daga wasu gungun ‘yan bindigan da kuma ba su abinci da sauran kayayyaki a lokutan bukata.

Su wane ne ƙungiyoyin  masu makamai da ke ingiza rikicin? Ƙungiyoyi nawa ne kuma yaya ne girman yawancin su? Su waɗannan kungiyoyi manya-manyan sana’o’in aikata laifuka ne kowannensu ke karkashin jagorancin wani mashahurin shugaba? ko kuwa akwai wasu ƙananan ƙungiyoyin masu aikata laifuka mai zaman kan su da yawa wanda ba su amincewa da jagoranci na tsakiya ba?

Nigerian Motorbike

Babura a Arewa maso Yammacin Najeriya. (Hoto: Jeremy Weate)

ADEBAJO: Samun ainihin ƙidayan na da wuya Kwamitin binciken da gwamnatin Zamfara ta kafa ya kiyasta cewa akwai sansanonin ‘yan bindiga akalla 105 a cikin jihar da kewaye inda ‘yan bindigar ke kaddamar da hare-hare. Galibin kungiyoyin sun fito daga Zamfara ne, kuma suna gudanar da ayyukansu daga wasu dazuzzukan da ke da hanyoyin haɗe da kuma da kuma ƙofar shiga  tsakanin Jihohi da dama, wanda ke ba su damar tafiya cikin walwala. Zamfara tana iyaka da jihohin Arewa maso Yamma da dama: Sakkwato, Kebbi, Niger, Kaduna, da Katsina. Wani mai bincike ya samu damar rubuta kungiyoyin ‘yan bindiga 62, akasari a Zamfara, tare da yawan maikatansu, tsakanin mutane kaɗan kamar 28 zuwa sama da 2,500. Wasu daga cikin manyan shugabannin ‘yan bindigan su ne Bello Turji Gudde, Halilu Sububu, Shehu Rekep, da Abubakar Abdullahi (wanda aka fi sani da Dogo Gide, wanda aka ce an kashe shi). Ƙungiyoyin suna  zaman kansu ba tare ba amma suna da tasiri daban-daban akan sauran ƙungiyoyi dangane da girma da kuma ƙarfinsu. Wannan ne ya sa zai yi wuya duk wata tattaunawa da shugaban kungiyar guda ta yi tasiri sosai a kan yanayin tsaro gaba daya.

RUFA’I: A tarihance akwai tarwatcecen ƙananan ƙungoyiyi ‘yan bindiga a tsakanin jihohin Zamfara da Kaduna. Shugabanni daban-daban sun mallaki yankuna daban-daban don magance saɓani tsakanin kungiyoyin, amma  ƙungiyoyin da ke  ƙarƙashi waɗannan shugabannin yakin suna da ɗan ‘yancin cin gashin kansu. Don haka jihohin Niger da Kaduna suna a ƙarƙashin Abubakar Abdallahi. Katsina ta kasance a ƙarƙashin marigayi Auwalun Daudawa da Dangote Bazamfare. Gabashin jihar Sakkwato na a ƙarƙashin ikon Turji ne. Kuma akwai shugabanni masu da yawa adawa da juna a jihar Zamfara.

Ayyukan ‘yan bindiga a Zamfara

Gari mai nisa a jihar Zamfara. (Hoto: Osinowo Oluwaseun Omotayo)

A tarihance, matsalar ‘yan bindiga ta Arewa maso Yammacin Najeriya ta fara ne daga Zamfara musamman a sakamakon yadda ake gudanar da harkokin mallakar filaye a farkon shekarun 2000 wanda manyan Hausawa suka amfana a bayan cin zarafin makiyaya. Yankunan dazuzzukan jihar Zamfara na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa dindindin ayyulan ‘yan bidiga a ƙarshe,   ya sami tushin kafawa. kuma suna gudanar da sana’o’i hakar da zinare da hannu   a Zamfara tare da yin amfani da iyakokin kasa da kasa ta Nijar don cin gajiyar safarar makamai da muggan kwayoyi.

A cikin shekarar da ta gabata, yawancin waɗannan ƙungiyoyin da a daa ke hamayya, a baya sun fara haɗin gwiwa da juna don yakar abokan gaban su, wato ƙungiyoyin kare al’umma da gwamnati a yayin da matakan dakile ‘yan bindiga (katsewar sadarwa, hana man fetur, da hana babura) suka fara aiki. Wannan haɗin kai ya baiwa kungiyoyin damar musayar bayanai kan yanayin tafiyan jami’an tsaro da kuma haɗa karfin makamai da maikatnsu a wajen kai da hari ga manyan kauyuka da garuruwan da aka fi tsaro. Wannan lamari ne mai tayar da hankali, amma ba a san ko za ta ci gaba ba don a kasancewan tarihi, ’yan bindigan ba sa wasa da ‘yancin kansu kuma sukan yi fadace-fadace a kan yankunansu.

Menene waɗannan ƙungiyoyi suke so?

ADEBAJO: A yawanci, kudi da dacewa. Ƙungiyoyin suna samun kuɗi daga hanyoyi daban-daban: sata daga mutanen gida (kudi, kayayyaki masu daraja, dabbobi), karɓan tara daga al’umma (don amfani da gonakinsu ko kuma don ba da kariya alal misali daga hare-hare),  ko ta hanyar biyan fansa daga mutane da gwamnatoci.   Har su ma, a wasu lokuta, su kan kwace filayen noma masu albarka da  karfi sai ’yan ƙungiyansu su yi noma da kansu.

‘Yan bindigan sun koka a wasu hirarrakin da aka masu, sun ce gwamnati tana masu wariya da kuma hana masu abubuwan more rayuwa kamar ilimi da kiwon lafiya. Sun yi zanga-zangar nuna wariya a matsayinsu na Fulani. Amma ayyukan aikata laifuka da ta’addanci na ‘yan bindigan, galibin ayyukan ta kasuci ne,  maimakon siyasa ko kabilanci. Wasu samaruka sun bayyana yadda suka shiga gungun ‘yan bindigan bayan da su kansu ‘yan bindigan suka rutsa da su har suka yi asarar komai da komai. We still do not see any major collective bargaining power as is the case with Boko Haram in the North East. Cin zarafi shine tsarin aikin su na yanzu.

RUFA’I: Tashin hankalin da aka yi a Arewa maso Yamma, a farko rigingimun filaye a sakamakon lalacewar muhalli shi ya kawao wannan, karuwar yawan jama’a, musamman cin hanci da rashawa na gwamnati a game da haƙƙin ƙasa wanda ya amfanar masu haɗin gwiwar siyasa da cin zarafin makiyaya wanda suka gan cewan an toshe hanyoyin shanu da wuraren kiwo na tarihi. Amma a lokacin da gungun ’yan bindigan da aka ɗauke su daga cikin makiyaya masu takaici suka fara kai farmaki ga al’ummomin manoman, suka gane cewa suna da ƙarfi,  ƙarfin hali, da kuma iya afkawa waɗannan al’ummomi yadda suka ga dama, sai tashin hankalin ya dauki wani sabon salo na tunzura jama’a saboda dalilai na tattalin arziki. Wasu sun zama ‘yan mahara na cikakken lokaci. Yanzu tashe-tashen hankulan asalin ayyukan laifi ne wanda ke haifar da riba ta tattalin arziki ne kawai.

“Yanzu tashe-tashen hankulan asalin ayyukan laifi ne wanda ke haifar da riba ta tattalin arziki ne kawai.”

Amma, sabbin matakan da gwamnatin ta ɗauka na ƙara farfaɗo da ƙorafe-ƙorafen kabilanci a tsakanin Fulanukan yankin da suke ganin kamar ana musu wariya mai rashin adalci ba, tare da matakan  tsare-tsare na gwamnati da ke niyya a kan mu kaɗai Wannan ra’ayi yana taimaka wa ƙungiyoyin a wurin ɗaukin matasan maza waɗanda waɗannan ka’idojin suka shafi rayuwarsu. Haka kuma yana taimaka wa gungun ‘yan daba wajen hada kai tare da kulla kawance a ƙarƙashin tutar kare Fulanuka. Duk da cewa har yanzu ’yan bindigan suna kai hari ga Fulanuka masu kiwon dambobi kuma da yawa daga cikin ’yan kungiyar ba sa ma jin harshen Fulatanci.

A waɗanne hanyoyi ne matakan tsaro na yanzu ke aiki kuma ta waɗanne hanyoyi ne ba ta aiki ba? Menene ya yi aiki a lokacin da ta wuce?

ADEBAJO: Babu shakka amsar tsaro na yanzu ba ta yi daidai da tssananin barazanar ba. Babu isassun jami’an ‘yan sanda a kasance, kuma waɗanda ake da su ba su da isassun kayan aikin. An shimfida sojojin kasar sosai har ma sun kaasa. Akwai kusan jami’an ‘yan sanda 334,000 a kasar, amma an kiyasta cewa kusan rabin su ne waɗanda aka tura a matsayin masu gadin da makamin  ‘yan siyasa ko masu kuɗi da za su iya biya don wannan hiɗiman. Wannan yana barin wani juz’in ‘yan tsaro don kare sauran jama’a. A kwanan nan, Gwamnan Katsina ya koka da cewa jami’an ‘yan sanda a jihar sa ba su kai 3,000 ba.

Kokarin da aka yi a lokacin da ya wuce na sasanta yarjejeniyar zaman lafiya da shirye-shiryen yin afuwa ga ‘yan bindiga a wurare kamar Zamfara ya ci tura Duk da cewa an samu nasarori da farko, ba da jimawa ba wadannan tsare-tsare sun wargaje, inda gwamnonin suka nuna rashin jin ɗaɗinsu da sake bullar hare-hare da tabarbarewar tsaro. Waɗannan yarjejeniyoyin ba su yi nasara ba sau da yawa saboda  rashin jagoranci na ƙungiyoyin ‘yan bindigan  da kuma kasancewar ƙungiyoyi da yawa masu zaman kansu.

Har ila yau, martanin tsaro yana buƙatar samun goyon baya ta hanyar sa ido da kuma aikin  ‘yan tsaro ​na al’umma. Hakan na buƙatar gina amincewar jama’a da huƙumomin tsaro, da ingantawa da kuma tantance bayanan tattara bayanai da darussa, da samun isassun hannaye masu inganci a cikin jami’an tsaro da na soja don bin diddigin bayanan sirri da aka samu. Akwai misalan kwamandojin soja na musamman waɗanda suka yi hulɗa da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai na al’umma kuma suka raka ma’aikatan su da suka kai a kan sansanonin ‘yan bindiga a cikin dazuzzuka. Lokacin da al’ummar yankin suka ga irin wannan sadaukarwar, sun ƙara sha’awar yin aiki da su da kuma samar musu da bayanan tsaro. Amma sai a sake canza wa waɗannan mutane aiki kuma waɗanda za su maye gurbinsu, sau da yawa, ba su dace ba.

Bangon garin Kaduna. (Hoto: Allan Leonard)

RUFA’I: Matakan da gwamnati ta ɗauka a baya-bayan nan sun sa ‘yan bindigan sun yi gudu na ɗan lokaci, amma sun daidaita kuma a zahiri sun yi amfani da yanayin a yanzu. Suna sadarwa da juna ta wayar kumbun ɗan adam, a yayin da a sakamakon toshen hanyoyin sadarwar wayar hannu, al’ummomin sun rasa yadda za su iya sadarwa da jami’an tsaro da kuma sabunta su game da hare-haren ‘yan bindiga da ke gabatowa. Haka kuma takunkumin hana zirga-zirga yana haifar da tashin farashin kayayyaki da kuma cutar da al’ummomin karkara a sakamakon haka. ‘Yan bindigan suna neman ƙarin haraji don sayan man fetur da ta yi tsada wanda a zahiri sune suka ƙara farashin da kansu. Wannan yana ƙara talautar da al’ummomin da ‘yan bindidan za su iya samun sabbin ma’aikata daga gare su.

Gwamnatin tarayya ta aika da ƙarin runduna zuwa yankin, amma har yanzu suna fama don an miƙe su da tsanani sosai, da kuma cewan an tura da yawan su zuwa yankin Arewa maso Gabas domin yakar Boko Haram. A galibi, sojojin suna zama a garuruwa masu garkuwa, da kuma sansanin soja, kuma da kyar su ke shigan yankin al’ummomin inda aka san  waɗannan kungiyoyi ‘yan bindigan da shugabanninsu wuraren da kowane yaro zai iya nuna su. Hare-haren da sojojin ke kai wa a lokuta da dama kamar suna kai wa makiyaya hari ne kawai, suna tsoratarwa da tarwatsa da su, wanda hakan ke ƙara saka al’ummar makiyaya a cikin talauci. Hare-haren jiragen sama ba a lokuta mai dama ba su da amfani, kuma da  hadari saboda ‘yan bindigan na amfani da mutanen kauyukan karkaran a matsayin garkuwar mutane, wannan yana nufan cewa da wuyan ware su don kai musu hari.

Kungiyoyin ‘yan banga al’umma suna da ƙarin ganuwa a yankin Arewa maso Yamma. Dangane da tashin hankalin da aka samu tun farko, waɗannan kungiyoyi sun sha kai wa Fulanuka hari ba ba tare da nuna bambanci ba kuma ya kara dagular da lamarin. Halayen wuce gona da irin ’Yan Bangan Sakai zuwa ga makiyaya shine farkon tashin kungiyoyin ‘yan bindiga na cikakken lokaci a yankin tun daga shekarar 2011. ‘Yan banga da yawa suna yi maganganu a fili kan kyamar Fulani a matsayin yanayi kamar Fulanuka wasu barazana ne da za a magance da su da tsauri. Don haka, cin zarafi na ƙungiyar da martani ga ƙungiyoyin masu laifin na da yuwuwar rikiɗe zuwa faɗaɗa rikice-rikice tsakanin al’ummomi.

“Wata irin da zai iya yiwuwa shi ne Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar-Hula a Arewa maso Gabas, wanda zai taimaka wajen samar da tsaro na dindindin ta hanyar horarwa, biyan su kuɗi, da kuma kula da ‘yan bangan ga tsarin aiki na hukuma.”

Ana iya fahimtar amfani da mayakan sa kai don kare al’umma saboda ƙarancin kasancewar tsaro, amma ƙungiyoyin ‘ƴan banga kamar “ ‘Yan Sakai” ba bisa ƙa’ida ba ne a fasaha, ba a horar da su ba, kuma ba a dora musu alhakin abin da suka aikata ba. Manufofin gwamnati na jihohin Arewa maso Yamma yankin ba ya daidai da halinsu ba, suna lilo tsakanin tallafa musu a kaikaice da haramtawa da la’antarsu. An san manyan  ’yan siyasa  amfani da su don daidaita koke-kokensu. Ana bukatar tsarin da ya dace da tsarin da zai dakile cin zarafi da waɗannan ƙungiyoyi ke yi a matsayin ‘yan bangar Hausawa kuma suna mai da rikicin ta zama ta kabilanci. “Wata irin da zai iya yiwuwa shi ne Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar-Hula a Arewa maso Gabas, wanda zai taimaka wajen samar da tsaro na dindindin ta hanyar horarwa, biyan su kuɗi, da kuma kula da ‘yan bangan ga tsarin aiki na hukuma.”

Shirye-shiryen afuwa na da damar yiwuwa saboda wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindigan suna bayyana cewa suna son zaman lafiya. Shirye-shiryen haɗin kai ta yin afuwa da ke haɗa da aiwatarwa mai kyau suna ba da yana gabatar da zaɓi na zahiri don in ba haka ba, zai yi wuya a shawo kan waɗannan ƙungiyoyi a yanzu da yawancin ƙungiyoyin sun yi kane-kane a cikin al’ummomi kuma suna aiki a matsayin matsayin masu mulki a inda gwamnati ba ta nan ba. Ƙoƙarin da aka yi a wajen yin afuwa a lokacin da ta gabata ya gaza saboda sun shafi Jiha ɗaya kawai kuma ba a haɗa kai da ganin cewan an gama ba. Sun kasance yarjejeniyar musafaha da ta ruguje Ƙarkashin damuwa.  Harin sojan da aka yi a kasa wanda a zahiri ya nemi kamun da kuma hukuntar da shugabannin ‘yan bindigan tare da ingantaccen shirin yin afuwa na iya fara haifar da sakamako.


Ƙarin bayanai