Ƙungyoyin Ƴan Bindiga sun Kaurar da kuma Rush Arewa maso Yammacin Najeriya

Kungiyoyin ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na kara yin barna, inda suka ci gaba da yin garkuwa da jama’a, suna kwace muhimman gonakin hatsi, da kuma haifar da gudun hijirar cikin gida.


Danna nan don cikakken taswira.

Rikicin kungiyoyin ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ya haifar da rashin zaman lafiya a wannan yanki da ke da kabilu daban-daban mai samar da hatsi da ke da kusan mutane miliyan 60. Rikicin da wadannan kungiyoyin ƴan bindiga, da aka fi sani da suna “‘yan bindiga” ke aikatawa, na kan hanyar mayar da shekarar 2024 a matsayin shekarar rashin tsaro mafi muni a tarihin baya-baya na yankin. Aukuwar tashe-tashen hankula 1,380 da asarar rayuka 3,980 da aka yi hasashe na shekarar sun zarce matakin da ba a taɓa samuwa ba da aka fuskanta a 2022 wanda raguwa ya biyo baya a 2023. Yanzu asarar rayuka da aka alakanta da ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma sun zarce waɗanda aka alakanta su da kungiyoyin masu kaifin kishin Islama, wani sauyi da aka lura tun 2021.

An kimanta cewa kashi 84 cikin ɗari na asarar rayuka da aka alakanta da ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma sun tattaru a Jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna— wanda ya mamaye tsakiyan yankin. Waɗannan hare-haren ya haɗa da fakon manyan birane, ciki har da birnin tarayya Abuja, wanɗa ya ninka adadin asarar rayuka biyu (zuwa 112). Ko da yake yana tasowa, wannan har yanzu yana nuna kashi 3 ne kawai na jimillar yankin. Karuwar rikicin da ya barke a kananan hukumomi ya sa an rufe kananan hukumomi uku da kauyuka da garuruwa tara na ɗan lokaci a jihar Zamfara kadai.

Bisa manufar shawo kan hanyoyin samun kudaden shiga, wadannan kungiyoyin ƴan bindiga na barazana ga al’umma ta hanyar fashi da makami a kan tituna, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, satar shanu, da ayyukan noma da ma’adinai. Wadannan kungiyoyi masu dauke da makamai sun sace tare da kashe fararen hula kimanin 9,200 a yankin tun daga shekarar 2019 lokacin da kungiyar ƴan bindiga suka fara haɓaka. A cikin haka, sun lalata daruruwan kasuwanci, tattalin arziki, da ayyukan noma.

Akwai manyan kungiyoyin ƴan bindiga sama da shirin da huɗu da kuma daruruwan kananan ƙungiyoyi, wadanda ke aiki a karkashin shugabanci da tsari daban-daban a fadin jihohi shida (da babban birnin tarayya da ke kewaye da Abuja). Alkaluma sun nuna cewa akwai sama da ƴan fashi 30,000 da ke aiki a yankin. Duk da cewa a wasu lokuta sukan yi kira ga Allah a lokacin hare-hare ko kuma a lokacin da suke yin faifan bidiyo na farfaganda, kungiyar ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma ba sa nuna wariya ga abin da suke yi bisa addini.

A wani bangare na dabarunsu na tashin hankali, kungiyoyin ƴan bindiga a yankin sun kara koma zuwa kwace gonaki, wanda ya shafi noma kai tsaye. Jihohin yankin Arewa maso Yamma suna da kaso mafi tsoka na gidajen noma a Najeriya, wadanda suka hada da Kano (na ɗaya), Kaduna (na biyu), Katsina (na biyar), da Sakkwato (ta sha daya).

Kusan mutane 700,000 ne suka rasa matsugunansu a yankin Arewa maso Yamma saboda wannan rashin tsaro.

Sauyin Dabaru

Da farko wadannan kungiyoyin sun shiga aikata miyagun laifuka ta hanyar satar shanu da kuma yin garkuwa da mutane amma daga baya suka koma yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa tare da kwace ayyukan gona da ma’adinai.

Don magance raguwar tsabar kuɗi daga sace-sacen ɗaidakun mutane, ƴan bindiga sun ƙara rikiɗe zuwa sace-sacen jama’a, suna fakon sama da mutane 80 ko 100 a lokaci ɗaya, yawanci a makarantu ko taron al’umma. Adadin sace-sacen jama’a (inda ake sace mutane biyar ko fiye a lokaci guda), da kuma adadin wadanda aka sace, ya karu a hankali tun daga shekarar 2019. A shekarar 2024, adadin mutanen da aka sace a irin wadannan hare-haren ya ninka biyu zuwa fiye da mutum 7,400. Sace-sacen jama’a a kalla guda daya na faruwa a kowace rana a kasar cikin shekarar da ta gabata. Yankin Arewa maso Yamma ya fi fama da matsalar wanda ke da kusan kashi biyu bisa uku na adadin wadanda abin ya shafa idan an kwatanta da sauran yankunan a hade.

Har ila yau, sace-sacen jama’a na jan hankalin ƴan jaridu da kuma, gwamnati, wanda ta fadada hanyar da za a iya biyan kudin fansa. Gwamnati ta dage cewa ba ta biyan kudin fansa, amma akwai shaidun da ke nuna cewa ta ci gaba da yin hakan, musamman idan wadanda abin ya shafa ƴan makaranta ne.

Wadannan dabaru da sauran su sun talautar da al’ummai tare da rufe harkokin tattalin arziki da siyasa a sassan yankin Arewa maso Yamma, lamarin da ya sa ake samun wahalar samun kudin fansa. Wannan ya haifar da firgici a yankin, wanda ƴan bindigan ke amfani da su ta hanyar sanya harajin “kariya” a kan al’ummomi. Wasu kauyuka a Sakkwato da Zamfara, bayan da suka rasa kwarin gwiwar cewa gwamnati za ta iya kare su, suna biyan kudaden kariya ga ƴan bindigan da suka kai miliyoyin nerori (kwatankwacin dubban daloli). Ana kai hari wa waɗanda suka gaza biyan kudi.

Harin noma na farko ya faru ne a watan Yulin 2022 a jihar Zamfara, lokacin da ƴan bindiga suka kai hari wata gona suka kashe manoma 11. Tun daga wannan lokacin, al’adar ta haɓaka cikin sauri. A wasu lokutan kuma, ƴan bindigan na dora wa manoma haraji a matsayin wata hanya ta kara samar da kudaden shiga. A yayin da wannan al’adar tana nan tun tuni, ta ta’azzara a cikin shekaru 2 da suka wuce inda aka samu yawaitar adadin da ake samun wadannan karɓe-karɓen kudade—wanda ya zarce abin da mafi yawan manoma za su iya tarawa, wanda ya kai su ga munanan hare-hare da sace-sace.

Hakazalika ƙungiyoyin ƴan bindiga suna tilastawa mutanen ƙauye zaman ma’aikata a gonakinsu da bindiga.

Hakan ya sa manoman da dama sun bar gonakinsu. Yanzu haka dai kungiyoyin ƴan bindiga sun kafa sansanoni a lungunan jihohin Zamfara, Sakkwato, da Katsina, inda suka kori mazauna yankin tare da shugabantar ayyukan noma. Hakazalika ƙungiyoyin ƴan bindiga suna tilastawa mutanen ƙauye zaman ma’aikata a gonakinsu da bindiga. Shahararren shugaban ƴan bindiga, Dogo Gudale na Zamfara, ya shahara wajen amfani da dabaru biyun.

Wasu daga cikin ƙwararrun shugabannin ƴan bindiga sun koma aikin haƙar zinari ba bisa ƙa’ida ba. Wannan ya biyo bayan sauyin da aka yi a baya daga satar shanu zuwa garkuwa da mutane tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, sakamakon raguwar ribar da ake samu na tsohon salon aikata laifuka. Waɗannan ƙungiyoyin galibi suna kwace ayyukan hakar ma’adanai. Misali, shugaban ‘ƴan bindiga Halilu Sububu, yana kula da wuraren hakar ma’adanai a yankin Bagega da ke Zamfara kuma ya sace da mutanen kauyen domin yi masa aiki. Sani Black ya dauki wannan tsarin a al’ummar Tunani da Daka na Zamfara. Kamar yadda ake yi a gonaki, waɗannan ƴn bindiga na iya wanzar da masu hakar ma’adinai ta hanyar neman wani kaso na ribar da suke samu daga ayyukansu.

Haka kuma ana samun karuwar kungiyoyin ƴan bindiga suna kutsawa cikin al’umma tare da kashe mazauna garin tare da kona gidajensu saboda ƴan bindigan sun yi imanin al’ummar na bayar da bayanan maboyarsu ga jami’an tsaro.

Gasa kan rashin isashen albarkatu ya haifar da karuwar rikice-rikice a tsakanin kungiyoyi ƴn bindiga daban-daban. Wannan ya hada da Kachalla Dankarami Gwasa da marigayi Sani Dangote da Bello Turji. Haka kuma an samu labarin faɗa tsakanin Ansaru da sansanin Dogo Gide da ke yankin Birnin Gwari a Kaduna, inda rahotanni suka ce Ansaru ya kwace aikin hakar ma’adinan Gide tare da yin artabu da dakarun sa.

Karuwar Lamarin Agaji

Hare-haren da kungiyoyin ƴan bindiga ke yi ya sa an sace ma’aikatan lafiya da dama, an wawashe kayayyakin kiwon lafiya, da kone-kone ko mamaye cibiyoyin kiwon lafiya da dama a jihohi kamar Katsina, Kaduna, da Zamfara. A wasu lokuta, ƴan bindiga suna kai hari ga waɗannan cibiyoyin kiwon lafiya don satar kayan aikin jinya don kula da ƴan uwansu ​​marasa lafiya lokacin da suka sami rauni a hare-hare.

Har ila yau rashin tsaro ya tilasta rufe wasu wuraren saboda haɗarin da ke tattare da ma’aikatan lafiya. Kusan shekaru 2 kenan da kananan hukumomin Zurmi, Maru, Bungudu, Tsafe, Birnin Magaji, Gusau ta Gabas, da Shinkafi ba su yi aiki ba, kuma samun kulawar lafiya a matakin kananan hukumomi a wadannan al’ummomi ya bace. Yanzu, lokacin da mutanen yankin Arewa maso Yamma ke bukatar kulawar lafiya, yawanci ba su da zaɓi sai dai su yi tafiya zuwa babban birnin karamar hukumar, babban birnin jihar, ko ma wata jiha mai makwabtaka.

A kananan hukumomin da aka ambata a baya, an rufe makarantu sama da shekaru 2 saboda tabarbarewar tsaro da ayyukan ƴan bindiga ke yi. A jihar Zamfara kadai makarantu 168 sun kasance a rufe. Hakanan ƴan bindiga suna gudanar da bukukuwa ko taro a makarantun da aka kora.

Victims of bandits outside a health clinic in Sokoto, Nigeria

Wasu da ƴan bindiga suka kashe a wajen wani asibiti a Sakkwato, Najeriya. (Hoto: AFP / Pius Utomi Ekpei)

Rashin zaman lafiya da kungiyoyin ƴan bindiga ke haddasawa shine ke da alhakin kashi 100 bisa 100 na gudun hijira a jihohin Zamfara da Neja, kashi 87 a Sakkwato, kashi 84 a Katsina, da kashi 50 a Kaduna.

Wannan kaura yana da tasiri kai tsaye kan samar da abinci, domin noma shi ne tushen tattalin arziki a yawancin jihohin nan. Har ma taken Zamfara ya kasance “noma abin alfaharinmu ne.” Filayen noma masu faɗi sun kasance ba za a iya iso su ba ko kuma an ƙyale su saboda ƙaura, wanda ke samar da kayan aiki kaɗan kaɗan. Inda mutane za su iya noma, wani kaso mai tsoka na girbin su yana zuwa ga ƙungiyoyin ƴan bindiga.

Tasirin kayan masarufi yana haifar da hauhawar farashin abinci da kuma karancin abinci. Hakan ya zamar da Najeriya ƙasa mai mutanen da ke fama da karancin abinci fiye da kowace kasa a Afirka. Alkaluma sun nuna cewa a kalla mutane miliyan 13.5 ne ke fuskantar matsalar karancin abinci a yankin Arewa maso Yamma, ciki har da 460,000 da ke fuskantar matsalar karancin abinci.

Dorewar Kasancewar Tsaro

Karuwar tashe-tashen hankulan ƙungiyar ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma na da nasaba da gazawar jihohi da gwamnatin tarayya wajen daidaita kokarinsu na ganin an tabbatar da tsaro – wanda hakan zai ba da damar masu aikata laifuka su yi amfani da su.

Karuwar tashe-tashen hankulan ƙungiyar ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma na da nasaba da gazawar jihohi da gwamnatin tarayya wajen daidaita kokarinsu na ganin an tabbatar da tsaro – wanda hakan zai ba da damar masu aikata laifuka su yi amfani da su. Lokacin da sun kasance isassu, sojoji sun sami damar dawo da iko a yankunan da ake gwabzawa. Hakika, asarar rayuka daga yake-yake tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindiga ya yi sakamakon kashe 56 bisa ɗari na asarar rayuka da ake alakanta da ƴan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya. Kalubalen shi ne dorewar wannan kasancewar saboda akwai bukatar jami’an tsaro a duk fadin yankin—da kuma a sassa daban-daban na kasar.

Martanin tsaro galibi suna sannu a hankali ko babu su a cikin al’ummomi masu nisa. Wasu wurare masu mahimmanci ba su da wuraren bincik ababen hawa ko ofisoshin ‘yan sanda. Hakanan ana jigilar jami’an tsaro daga wuri zuwa wuri saboda canzuwar al’amurra, wanda ke sanya wasu al’ummomi cikin haɗari. Magance wadannan karancin na ɗan lokaci na bukatar samar da dabarun kasa don fadadawa, ba da kudade, da horar da jami’an tsaro a matakin jihohi, rundunar ƴan sandan Nijeriya, da kuma sojojin Nijeriya. A halin yanzu, za a iya ɗaukar matakan fifiko a yankin Arewa maso Yamma.

Sake ba da fifikon tura jami’an tsaro don kare al’ummomi da ke cikin haɗari. Ya kamata gwamnatocin jihohi su tsananta kasancewarsu a cikin al’ummomin karkara. Samuwa da tura jami’an ƴan sanda da aka horar da su yana da daraja. Jami’an ƴan sandan da ke wurin kuma suka sami amincewar al’ummomin karkarar suna da mahimmanci wajen tantance barazanar da kuma mai da ingantattun martani. Hanya ɗaya da za a kara yawan jami’an ƴan sanda ita ce rage yawan jami’an ƴan sandan jihohi da aka tura su zama masu rakiyar manyan mutane maimakon kare al’ummomin da ke cikin haɗari. Daidaita wannan fifikon da ba da kwangila ga kamfanonin tsaro masu zaman kansu don kare manyan mutane zai yantar da jami’ai.

Fadada ayyukan soji da ke tafiyar da leken asiri. Ayyukan soji da ke amfani da leken asiri na iya kai yaƙin zuwa wuraren da ƙungiyoyin ƴan bindiga ke kasancewa, tare da ƙasƙantar da ƙarfin ƙungiyoyin su da kuma iya ɗaukar ayyukansu na cin zarafi a kan al’ummomin karkara. Wannan yana buƙatar sojojin su yi aiki kafada da kafada da ƴan sanda da ƙungiyoyin al’umma waɗanda suka fi sanin yanayin asali da na zamantakewa na yankin. Wannan tsarin haɗin gwiwar kuma zai iya iyakance asarar fararen hula daga ayyukan soja waɗanda za su lalata haɗin gwiwar ƴan ƙasa.

Ci gaba da jijjiga tare da aikin sintiri na manyan hanyoyin sufuri a sassan yankin da ƴan sanda, sojoji, da na farar hula na hadin gwiwa suka yi, ya rage rashin tsaro da kungiyoyin ƴan bindiga ke haddasawa, ciki har da satar mutane.

Ci gaba da kasancewa a kanana hukumomi. Ana cin mutuncin ƙungiyoyin ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma da rashin goyon bayan jama’a. Al’ummomin karkara na fuskantar zaɓin yin aiki tare da su ko jure harin. Jama’a za su yi maraba da ingantaccen kasancewar gwamnati don kada a tilasta musu su karbi kungiyoyin ƴan bindiga. Yin hakan zai bukaci fiye da jami’an tsaro, ciki har da shirye-shiryen gwamnati na ganin an magance asarar filayen noma sakamakon sauyin yanayi da kuma inganta rayuwa a wuraren da abin ya shafa ta yadda ba a bar wata kabila ko al’umma a baya ba.

Ƙarfafa tsarin doka. Adalci da bin doka na da matukar muhimmanci wajen dorewar tsaro a yankin Arewa maso Yamma. Wani muhimmin abu na ci gaba da kasancewar gwamnati da samar da amana shi ne tabbatar da cewa ƴan ƙasa za su iya dogaro da tsarin adalci mai aiki don warware takaddama. Idan aka aikata wani laifi, dole ne a sa masu laifin su fuskanci shari’a a cikin aminci da rashin son zuciya ba tare da la’akari da matsayinsu ko asalinsu ba. Rashin ingantaccen tsarin adalci na ba da damar rashin hukunci da aikata laifuka. Hakazalika rashin hukunci na sa mutane su ɗauki al’amura a hannunsu, wanda ke haɓaka halayen aikata laifuka. Hakanan tsarin doka mai aiki na samar da tushen ingantaccen shirin kwance damara a yankin baki daya, yana mai nuni ga masu guduwa cewa za a yi musu adalci, harda da gyarawa da yanke hukunci mai sauki.

Police in Kaduna State.

Ƴan sanda a jihar Kaduna. (Hoto: Allan Leonard)

Ƙirƙirar tsarin mayakan sa kai na tabbatar da tsaron ƴan ƙasa a cikin yankunan karkara. Bisa la’akari da karancin jami’an tsaro a halin yanzu, ana ganin tura dakarun mayakan sa kai na al’umma ya zama wajibi. Yayin da aka samu nasarori da wannan tsari a karkashin Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa a Arewa maso Gabas, yanayin karfafa gwiwar mayakan al’umma na tattare da haɗarin waɗannan kungiyoyi na zama barazana ga al’ummomi.

A kwanakin baya ne jihohin Katsina da Zamfara suka kaddamar da abin da suka kira Community Watch Corps and Community Protection Guards (Askarawan Zamfara). Haka kuma akwai Ƴan Banga a Kaduna da kuma jami’an tsaro na al’umma a Sakkwato. Duk da haka, an soki matakan saboda yadda suke nuna son kai a ɗaukan aiki, da rashin isassun horo, da rashin sa ido da kuma rikon amana. Ana zargin wasu mayakan al’umma da laifin nuna kabilanci, satar shanu, kone-kone, da kuma kisan gilla.

Ana bukatar tsauraran matakai domin dakile wuce gona da iri na kungiyoyin ƴan banga da ake zargi da kashe fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba saboda kabilarsu. Kungiyoyin ƴan bindiga suna amfani da kyamar Fulani da kai hare-hare don yada farfagandar cin zarafi tare da daukar mutanen da suke son daukar fansa ko kuma ganin laifi a matsayin hanyar fita daga kangin talauci da rikici ya haifar musu. Hare-haren wuce gona da iri da dakarun sa kai na al’umma ke kaiwa zai kuma sa sulhu ya zama mai wahala a lokacin da rikici ya wuce. Don haka waɗannan jami’an tsaron al’umma, dole ne a basu isassun umarni da kuma dora musu alhakin mutunta doka.

Rashin horon aiki da makaman da ake buƙata don dacewa da ƴan bindigar, ƙungiyoyin al’umma a lokaci guda sukan yi asara mai yawa a hannun ƙungiyoyin ƴn bindiga. Domin yin aiki yadda ya kamata a matsayin mai hana kai hare-hare a kan farar hula, ana buƙatar horar da mayakan al’umma yadda ya kamata, da samar da kayan aiki, da kuma tallafa musu don tunkarar maharan.

Mista Kunle Adebajo wani dan jarida ne da ya yi rahoto sosai kan rikicin ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma. Mallam Hamza Ibrahim ɗan jarida ne da ke Kano wanda ya bi diddigin yadda barazanar tsaro ke kara ta’azzara da kuma yadda ake tunkarar matsalar tsaro.


Ƙarin bayanai