English | Français | Hausa
Wani shiri na INTERPOL mai ƙasashe 21 da aka fi sani da Operation Jackal III da ke fakon kungiyar mujrimai Black Axe ta Najeriya, ya kai ga kama mutane 300 da ake zargi da kama wasu kadarorin da suka kai dala miliyan 3 a wani samame da aka kai a watan Yulin 2024. Duk da cewa nasara ce ga jami’an tsaro, da wuya matakin zai iya yin tangarda a ayyukan Black Axe, wanda ke da mambobi kimanin 30,000 a kasashe da dama da kuma kuɗaɗen da ake samu a duk shekara da aka kiyasta ya haura dala biliyan 5.
Da farko an kafa shi a shekarar 1977 a Jami’ar Benin da ke Jihar Edo a matsayin haɗin gwiwar ɗalibin Black Power na Afirka, Black Axe tun daga lokacin ya rikiɗe zuwa ƙaƙƙarfan ƙungiyar laifuka na ƙasa da ƙasa tare da ɓangarori a Amurka, Kanada, Italiya, Brazil, Argentina, Ireland, Hadaddiyar Daular Larabawa, Afirka ta Kudu, Faransa, Burtaniya, Spain, Portugal, da Netherlands da sauransu. Har ila yau, kungiyar na da kafa a kasashen yammacin Afirka, kamar Ghana da Cote d’Ivoire, kuma ana iya samun ta a can nesa kamar China, Japan, Malaysia, da Singapore.
Kuɗaɗen da aka samu daga aikata laifukan yanar gizo ya haifar da hadaddun hanyoyin halatta kuɗaɗen haram da suka mamaye duniya.
An san ƴan Black Axe (wanda ake kira Axemen) da tashe-tashen hankula da ta’addanci a Najeriya, da kuma yin fataucin miyagun ƙwayoyi, fasa-kwauri, garkuwa da mutane, da kuma kwace. Hakanan Axemen suna gogayya a kan yanki tare da ƙungiyoyin mujrimai masu hamayya—Kamar Maphites, the Supreme Eiye Confraternity, da Vikings—kuma ana tuhumar su da ci gaba da al’adar tashin hankali a birane, cin hanci da rashawa na siyasa, da rashin hukunta masu laifi. A Najeriya, an sami mutuwar kusan mutane 6,000 da ake alakanta da kungiyoyin ƴan daba a cikin jihohi 31 daga 2006 zuwa 2021.
A cikin ayyukanta a ƙasashen waje, membobin Black Axe suna aikata laifuka irin su fataucin miyagun kwayoyi, ƙwace, da sarrafa ma’aikatan jima’i. Sashen laifukan da suka fi samun riba na ƙungiyar, wato laifukan yanar gizo, ya ketare iyakokin ƙasashe kuma ana tunanin ya samar wa ƙungiyar dubunnan biliyoyin daloli. A farawarsu a matsayin “Yahoo Boys” masu aikata zamba ta hanyar imel, yawancin membobin Black Axe sun girma zuwa ƙwararrun masu aikata laifuka ta yanar gizo waɗanda suka ƙware wajen zamba cikin kasuwancin dubbai zuwa miliyoyin daloli. Sakamakon haka, kuɗaɗen da aka samu daga aikata laifukan yanar gizo ya haifar da hadaddun hanyoyin halatta kuɗaɗen haram da suka mamaye duniya.
Ingantaccen Tsari da Ayuka Daban-daban
Laifukan Yanar Gizo
INTERPOL ta bayyana Black Axe a matsayin daya daga cikin manyan masu aikata laifuka da ke da alhakin zamba ta hanyar yanar gizo a duniya. Axemen ta fara ne ta hanyar mayar da zamban da ake kira “419” (wanda, misali, Yariman Najeriyan da ba na gaskiya ba yana buƙatar kuɗi don samun gadonsa) zuwa intanet a tsakiyar shekarun 1990 zuwa 2000. A cikin shekarun 2010s, membobin Black Axe sun shiga cikin ƙarin nau’ikan zamba na yanar gizo, har da zamban imel na kasuwanci (BEC), zamba da ke yaudarar mutane su aika kuɗi ko fallasa bayanan kamfani na sirri. Misali, Axemen ta saci €91,000 (kimanin $98,000) daga wani kamfanin kera robobi na ƙasar Ireland ta hanyar kwaikwayon daya daga cikin dillalan su. Akwai wani makircin inda ƴan damfara sun fito a matsayin masu tallata kide-kide don damfarar dillali da ƙasar Spain Imprex €294,000 (kimanin $317,000).
Wadannan kudaden na iya zama ba komai ba ga manyan kamfanoni, ammaadadin na karuwa. Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta kama mambobin Black Axe 13 a shekarar 2019 da laifin satar sama da dala miliyan 10 ta hanyar aikata laifuka ta yanar gizo. Daga baya FBI ta kama wasu ma’aikatan Black Axe 33 wadanda suka sace sama da dala miliyan 17 ta hanyar amfani da zamban imel na kasuwanci (BEC) da sauran nau’ikan zamba ta yanar gizo a shekarar 2021. Mutum na iya tunanin cewa manyan kamfanoni na kasa da kasa suna da wayo sosai na guje wa irin waɗannan dabarun, amma ana tunanin Black Axe yana ɗaukar tsakanin dala miliyan 300-500 a kowace shekara ta amfani da zamba na imel na kasuwanci (BEC) a Arewacin Amurka kaɗai.
Kamar yadda wani mai lura ya ambata, Black Axe ya haura daga aikata “ƙananan zamba zuwa manyan zamba”, daga “masu sata daga aljihu zuwa ƴan fashin bankuna” ta amfani da irin hanyoyin yaudarar da suka yi amfani da su yayin aikata zamba na “419”.
Halatta Kuɗin Haram
Faɗin yanayin ayyukan laifuffukan yanar gizo na Black Axe ya haifar da wani kamfanin halatta kudin haram na duniya. Misali, idan Axemen ta damfari wani mutum a kasar waje, yawancin lokuta su kan umurci wanda aka damfara ya aika da kudin zuwa wani asusu na cikin kasar shi don gujewa ganowa cewa ɗan damfarar ɗan Najeriya ne. Hakanan ƙungiyar na amfani da ɗan tsakiya ko “mahaɗi” don tura kuɗin daga asusun ajiyar kuɗi zuwa gungun ƴan Black Axe masu satar kudi ba tare da jawo hankalin hukumomi masu kula da kudi ba. Da zarar sun karɓi kuɗin, ƴan Black Axe na rarraba kuɗin ta hanyar saka hannun jari daban-daban.
Wani shiri da ya shahara a Arewacin Amurka shi ne masu halatta kuɗin haram su sayi motoci su yi jigilar su zuwa Najeriya. Wata dabara kuma ita ce siyan gidaje, wanda ke kara tsadar gidaje da matse masu sayan gida. Hakanan ana iya saka waɗannan haramtattun kuɗaɗen cikin kasuwanci, wanda ke fi na kamfanoni masu bin doka wadanda ba su da damar samun wannan jari. Cryptocurrency—wanda ke ɓoye masu mallakar ta kuma ana iya aika nan take tsakanin asusu da asusu na dijital a duk faɗin duniya—shi ma muhimmin dabarar satar kuɗin Black Axe ne.
Black Axe masu halatta kudin haram da mahaɗan su na bunƙasa a cikin ƙasashe marasa tsattsauran ƙa’idodin kuɗi da sa ido. Daya daga cikin wadannan cibiyoyi ita ce kasar Ireland inda mahaɗi dan Najeriya Junior Boboye ya taimaka wajen safarar miliyoyin daloli wa Black Axe kafin kama shi a shekarar 2018. Wani wurin da aka fi so shi ne Hadaddiyar Daular Larabawa inda shahararren mai alaka da Black Axe Ramon Abbas ya fito fili ya tallata ayyukansa tare da ba da dukiyarsa a Instagram kafin kama shi a shekarar 2020. Wanda aka fi sani da “Hushpuppi,” Abbas ya yi aiki ne daga Dubai kuma ba wai kawai ya taimaka wajen wawure kudade wa Black Axe ba, har ma da Lazarus Group—shahararren ƴan gwanin kwamfuta na Koriya ta Arewa wanda ke da alhakin harin fansa na WannaCry a shekarar 2017. Duk da yake ba a bayyana kama mutane a ƙasar China (PRC) ba, sadarwar cikin gida ta Black Axe ta nuna cewa kuɗaɗenta na shiga cikin asusun banki a Hong Kong da babban yankin kasar China saboda “rashin sa idon ta a kan kudaden haram.”
Black Axe masu halatta kudin haram da mahaɗan su na bunƙasa a cikin ƙasashe marasa tsattsauran ƙa’idodin kuɗi da sa ido.
Ko da yake Black Axe masu halatta kuɗin haram sun gwammace yin aiki a ɓangarorin duniya marasa tsattsauran manufofin kuɗi, suna iya yin kasuwanci a ko ina kuma galibi suna ɓoyewa a sarari. An ɗaure Ikechukwu Amadi, mazaunin Mississauga, Ontario (Kanada), a shekarar 2019 saboda sa hannu a cikin shirin halatta kuɗin haram dala biliyan 5. An yanke wa Ghaleb Alaumary, shi ma wani attajiri mazaunin yankin Toronto hukumci a Amurka a shekarar 2021 saboda laifin wawure miliyoyin daloli da aka sace ta hanyar amfani da tsare-tsaren zamban tura kuɗi da na banki.
Tashe-tashen Hankula da Laifuka a Najeriya
A Najeriya, ba a san Black Axe a matsayin gungun gogaggun mujrimai ba, sai dai a matsayin kungiyar ƴan daba masu tayar da hankali. Hotunan gawar makiyansu na fitowa a kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta na zamani, mai ta da hankali da bacin rai a zukatan ƴan Najeriya a fadin kasar. A manyan garuruwa irinsu Legas, Fatakwal, da kuma birnin Benin, ƴan kasar na fuskantar barazanar tashin hankali, fyade, da karbar kudi daga ƴan kungiyar Black Axe da kuma haɗarin kasancewar su cikin rikicin kabilanci. An yi kiyasin cewa mace-macen da ke da nasaba da irin wannan tashin hankalin ya ninka sau biyu tun daga shekarar 2019. Wasu kuma suna damuwa cewa za a kashe ƴaƴansu ko kuma wata rana a shigar da su cikin kungiyar asirin.
Wannan damuwa ta samu asali daga cewa Black Axe da sauran ƙungiyoyin suna ɗaukar sabbin mambobi daga jami’o’i da makarantun sakandare. Wanda aka sani a cikin gida a matsayin kungiyar asiri, Black Axe ta shahara saboda ayyukanta na karɓar sabin mambobi cikin sirri, a lokacin da ake yawan yin mubaya’a a sume ko kuma a wasu lokuta a umurce su da su kashe wani ko ma dan uwa. Bayan an gayyace su, masu shiga ƙungiyar za su yi rantsuwa da Korofo, “wani allah gaibi,” don samun kusanci da duniyar masu sihiri da tsafi, wanda ƴan Najeriya ke tsoro da ki.
Da zarar an shiga ƙungiyar, yana iya zama da wahala a fita. Masu fita na iya fuskantar muguwar ramuwar gayya a hannun tsofaffin mambobi ko kuma su fuskanci hari daga kungiyoyin da ke gaba da ƙungiyansu na da, bayan sun yi watsi da kariyar kungiyar. Wasu kuma suna shiga ƙungiyoyin ƴan banga waɗanda ke haifar da tashin hankali mara iyaka ta hanyar yaƙar ƴan ƙungiyar.
Tsarin Ƙungiya
Black Axe na aiki a cikin tsarin ƙungiya sarƙaƙƙiya kuma mara kyau. A Najeriya, mutane sukan dauki Black Axe a matsayin mai kama da kungiyar iyayenta ta doka, Neo-Black Movement of Africa (NBM). NBM kungiya ce mai rijista da Hukumar Kula da Kamfanoni ta Najeriya kuma tana da mambobi sama da miliyan daya. Yayin da NBM ke ba da ɗimbin hanyoyin sadarwar zamantakewa da na ƙwararru kamar sauran ƙungiyoyin haɗin gwiwa, ƙungiyar ba shakka tana bunƙasa ta hanyar haramtattun kuɗaɗen Black Axe. Don haka mutum zai iya tunanin Black Axe a matsayin reshen masu laifi na NBM.
Cin zarafin ƴan Najeriya a ƙasashen waje wani muhimmin sashi ne na ayyukan Black Axe.
Har yanzu ba a san mafi yawan tsarin ƙungiyar Black Axe ba, kodayake akwai shugaban da ke kula da tsarin Black Axe tare da babban majalisar dattawa. Bayanan da aka bankado sun nuna cewa tsohon shugaban Black Axe, Bemigho Eyeoyibo, shi ne shugaban NBM. A aikace, Black Axe na gudanar da wata hukuma ta ƙasa da ta ƙunshi majalisar dattawa ta dabam da kuma majalisar zartarwa ta shiyya a ƙarƙashin jagorancin shugaba.
Hakan na jagorantar shugabannin shiyyar da ke gudanar da ayyuka a wasu yankuna. Akwai kimanin shiyyoyi 60 da suka mamaye kowace babbar karamar hukuma ta Najeriya. A ɓangaren kasa da kasa, an yi imanin akwai yankuna 6 a Arewacin Amurka, 2 a Kudancin Amurka, 7 a Asiya, 16 a Turai, da 4 a Afirka. Wana lokaci ana shirya shiyyoyin ƙasashen duniya ta ƙasa, wani lokacin kuma ta birni. Hakanan akwai ƙarin ayyuka na musamman: manyan firistoci suna tsara bukukuwa da yin layuka don ƙare membobin; mahauta suna tabbatar da ladabi da shirya hare-hare kan abokan hamayya; “masu sanarwa” suna kula da sadarwa; sai kuma “ihaze” suna aiki a matsayin ma’ajin rukunoni. A ƙarkashin su akwai jerin sojoji ko “streets” waɗanda ake amfani da su a matsayin ƴan ƙafa wajen aikata laifuka kuma ana bukace su da su biya kuɗi ga shugabannin saman su.
Tsarin ƙungiyar Black Axe na yunkurin kasancewa na cin zarafi a fagen aikata laifuka ta yanar gizo. Kamar yadda wani jami’in tsaro da ke bin diddigin Black Axe ya lura, Axemen “na iya aiki tare da wasu mutane a wani mako, [amma] mako mai zuwa suna aiki tare da wasu mutane daban.” Wani kwararre ya lura cewa “mutumin da ke jagorantar aiki guda [wa Black Axe] na iya canzawa ba tare da ɓata lokaci ba zuwa wani aiki na ƙasa da hakan a cikin wani aikin laifin [yanar gizo] na daban [… kuma wannan rashin matsayi ya mike] har zuwa tsarin biyan kuɗi, inda, sabanin sauran tsarin laifuka, kaso na ayyukan BEC na canzawa kuma ya dogara da muhimmancin kowane aiki.”
Ɓangarorin Black Axe na kasashen waje suna aikin zaman kansu kuma sau da yawa ba za su aika kudi ga hukuma ta kasa a Najeriya ba. Wannan ya yi sanadiyar tashin hankali a cikin kungiyar kuma ya sa kungiyar ta kasa ta sanya dokar hana daukar ma’aikata a Turai musamman a Italiya inda ƙungiyar mafia Cosa Nostra da Camorra ke ba da dama ga ɓangaren Black Ax na cikin gida suyi aiki a cikin yankinsu don musayar kaso a ribarsu.
Cin zarafin ƴan Najeriya a ƙasashen waje wani muhimmin sashi ne na ayyukan Black Axe. Lokaci zuwa lokaci, Axemen na tilastawa ko shawo kan ƴan ci-rani na Najeriya su shiga ayyukansu na halatta kuɗin haram. Wani lokaci hakan ya kunshi tilastawa ƴan ci rani su yin amfani da asusun ajiyarsu na banki domin karbar haramtattun kuɗaɗe. A wasu lokuta, masu ƙaura sun zama “alfadar kuɗi” na gaske waɗanda ke taimakawa wajen tura kuɗi ga masu halatta kuɗin haram. Hakanan a Kudancin Amurka ma Black Axe na amfani da ƴan ci-rani daga Najeriya da Venezuela wajen safarar hodar Iblis zuwa Najeriya da Turai ta jirgin sama. A karshe dai Black Axe ta tsunduma cikin harkar karuwanci da matan Najeriya ke yi, a matsayin wani bangare na harkar safarar jima’i a kasashen Italiya da Faransa.
Tsarin Ubangida a Najeriya
Black Axe na cin zarafin al’ummai, musamman samari, a Najeriya ma. A nan tana amfani da matasa, ƙananan mambobinƙungiyoyi, waɗanda aka sani da “streets,” don yin yaki a kan yanki, sarrafa kasuwannin haram, da satar mai daga bututun mai. An yi kiyasin satar man fetur a Najeriya ya samu dala biliyan 46 tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020. Kuɗaɗen da aka samu daga irin wadannan haramtattun ayyuka na baiwa shugabancin Black Axe damar shigar da kansu cikin tsarin siyasar Najeriya tare da kulla hanyoyin hada kan ubangida.
Kudaden da aka samu daga haramtattun ayyuka sun baiwa shugabancin Black Axe damar haɗa kansu a cikin tsarin siyasar Najeriya.
Rawar da wasu shugabannin Black Axe ke takawa wajen kula da ayyukan aikata laifukan Black Axe da kuma rayuwar siyasar Najeriya na nuna kalubalen bincike da gurfanar da Black Axe a Najeriya. Shaidar da gwanin kwamfuta “Uche” Tobias ya fitar ya nuna cewa Bemigho Eyeoyibo shi ne shugaban NBM da kuma shugaban Black Axe daga 2012 zuwa 2016. Ko bayan an sanar da hakan wa jama’a, an baiwa Eyeoyibo damar tsayawa takara a matsayin dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2019. An ruwaito cewa wani fitaccen Axeman, Tony Nwoye, ya wawure kuɗin gwamnati ya kai wa Black Axe, amma an bar shi ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar PDP a jihar Anambra. A karshe, fitaccen “Ubangida” na Jihar Edo, Tony Kabaka, wanda mamba ne na NBM da APC, shi ma ana tunanin yana da alaka da Black Axe.
Samar da goyon bayan ubangida kamar Kabaka na da matukar muhimmanci ga ƴan siyasa a Najeriya. Ubannin gida suna baiwa ƴan siyasa kudi da sauran tallafi don samar da goyon baya wa ƴan takara. Wasu kuma na iya amfani da ma’aikata daga ƙungiyoyin ƴan daba da mujrimai kamar Black Axe don tsoratarwa da tilastawa. Sakamakon haka, yaran siyasa na ba wa ubannin gida damar samun kuɗaɗen jama’a da karfin siyasa da zarar an zabe su.
Matsaloli da ke Cikin Tuhumar Black Axe
Yayin da INTERPOL ta samu nasarar fatattakar Black Axe a kasashen waje, yunkurin dakile Black Axe a Najeriya bai yi nasara ba. Gwamnatin tarayya ta kafa Dokar Hana Ayyukan Ƙungiyan Asiri da Makamantansu a shekara ta 2004, wacce ta zama wani tsari na dakile ayyukan ƴan ƙungiyan asiri. Haka kuma wasu jihohi da dama sun zartar da dokar da ta haramta ayyukan ƙungiyan asiri, inda rundunar ƴan sandan jihar Edo suka tura wata Runduna ta Musamman ta Yaki da Ƙungiyan Asiri. A shekarar 2021, gwamnan jihar Legas ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da za ta hukunta iyayen matasan da aka samu da hannu a ayyukan kungiyar asiri.
Wadannan manufofin sun nuna wani matakin niyar fuskantar Black Axe a siyasance a Najeriya. Yawancin ƴan Najeriya sun raina kuma suna jin barazanar kungiyoyin ƴan daba kamar Black Axe. Al’umma a fadin kasar nan sun jagoranci yunkurin haɗa kan cibiyoyin gargajiya, na ilimi da na addini domin kawar da samari daga aikata miyagun laifuka. Hakanan ƙungiyoyin ƴan banga sun kama waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar kuma suka mika su ga ƴan sandan yankin. Wannan yunƙurin ya haifar da dubban kananan kame. Duk da haka, al’adar rashin hukunta laifuka ta hanyar gurfanar da kungiyoyin mujrimai kamar Black Axe ta ci gaba ganin cewa yawancin manyan jami’ai, masanan shari’a, da jami’an tsaro a matakin jiha da tarayya ƴan ƙungiyar ne.
Al’adar rashin hukunta laifuka ta hanyar gurfanar da kungiyoyin mujrimai kamar Black Axe ta ci gaba ganin cewa yawancin manyan jami’ai, masanan shari’a, da jami’an tsaro a matakin jiha da tarayya ƴan ƙungiyar ne.
Ƙungiyoyi kamar NBM tare da Ƙungiyar National Association of Airlords and the Green Circuit Association (tushen ƙungiyar mujrimai na Supreme Eiye Confraternity da Maphites) na da miliyoyin mambobi. Ana iya haɗa kasancewa cikin ƙungiyoyin asiri na zamanin mulkin mallaka kamar Ogboni da Owegbe, waɗanda ke gaba da ƙasa, da kasancewa memba na ƙungiyoyi kamar Black Axe.
Don haka Najeriya ta hukunta kaɗan daga cikin su, har ma wani kwamishinan ƴan sanda a jihar Edo na cewa, “duk lokacin da muka kama ƴan kungiyar muka tsare su, sannan mu samu kira… [daga] mutane a matakin gwamnatin jiha, ƴan siyasa… dole ne mu ƴantar da su.” A halin yanzu, rashin sa ido, ƴan sanda da jami’an tsaro a matakin jiha sukan yi amfani da dokar hana ƙungiyan asiri wajen murkushe halastattun ƙungiyoyin dalibai da zanga-zangar matasa.
Darussa Daga Yakar Kungiyoyin Mujrimai A Wani Waje
Wataƙila Italiya ita ce ƙasa da ta fi cin nasara wajen tunkarar laifuka. A cikin 1982, Majalisar Italiya ta kafa Doka mai Lamba 416-bis na Kundin Hukunta Laifuka wanda ya ayyana ƙungiyoyin mafia da kuma kafa mafi ƙarancin hukuncin ɗaurin kurkuku ga waɗanda aka gano suna cikin irin waɗannan ƙungiyoyi. Har ila yau, kasar ta kafa Cibiyar Bincike ta Anti-Mafia Investigation Directorate (DIA), National Anti-Mafia and Anti-Terrorism Directorate (DNA), tare da Dokar Yaki da Mafia a shekarar 2011 wanda ya ba wa jami’an tsaro damar tunkarar tushen kudin ayyukan mafia ta hanyar ba ƴan sanda damar kwace kuɗaɗe da abubuwa masu daraja da aka sace cikin sauki.
Italiya ta kuma dogara ga ƙngiyoyi masu zaman kansu(ciki har da kamfanoni masu zaman kansu da Coci) da ƙungiyoyin jama’a kamar Addopizzo da Libera don kare waɗanda mmafia ke fako shafa da masu leken asiri, tallafawa kasuwancin da cin zarafi ya shafa, da sake rarraba kadarorin da aka kwace wa al’ummomi. Wadannan ayyukan sun lalata tallafin da kungiyoyin masu aikata laifuka suka samu a da a kudancin kasar kuma sun taimaka wa Italiya wajen shawo kan “al’adanta na mafia” mai tarihi.
A wasu lokuta, an sami ci gaba a yaki da aikata laifuka saboda haɗin gwiwar kasa da kasa. Alal misali, a shekarar 2006, gwamnatin Guatemala da Majalisar Dinkin Duniya sun kafa Hukumar Yaki da Rashin Hukunta Laifuka ta Duniya a Guatemala (CICIG), da ke dangana a kan ikon shari’ar Guatemala wajen fuskantar cin hanci da rashawa na siyasa da kungiyoyin ƴan daba. Hukuma ta CICIG ta yi wasu manyan nasarori: ta aiwatar da manyan shari’o’i da dama, ta kuma gano ƙungiyoyin mujrimai guda 70, kuma mai yiwuwa ta kawar da mutuwar mutane 20,000 zuwa 30,000. Shugaban kasa Jimmy Morales ya kawo karshen CICIG a shekarar 2019 bayan da Hukumar ta fara binciken kuɗaɗen kamfen neman zabensa. Tun daga lokacin ne wasu suka caccaki hukumar ta CICIG da gaza yin gyara a fannin shari’a a Guatemala, inganta aikin binciken ƴan sanda, da kuma karfafa karfin masu gabatar da kara na gwamnati don murkushe manyan laifuka.
Sauran tsaruka sun jaddada baiwa mahukuntan shari’a na jihohi kayan aikin da suka dace don taimaka musu wajen fuskantar manyan laifuka da kansu. Kafin a kawo karshen gwamnatin mulkin sojan Mali a shekarar 2023, rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, MINUSMA, ta kafa Sashen Shari’a kan Ta’addanci da manyan Laifukanda ke Tsakanin Kasa da Kasa da aka kafa da nufin baiwa masu gabatar da kara da jami’an tsaro na Mali tallafin dabaru da bayanan da ake bukata don gurfanar da masu laifi, ƴan ta’adda da masu daukar nauyinsu na siyasa.
Wani yunƙuri na shekarar 2024 a Haiti, wanda Ofishin Babban Kwamishinan Ƴancin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya goyi baya, ya yi nasarar ƙirƙirar sabbin “tsarurrukan shari’a.” Waɗannan hukumomin shari’a ne waɗanda suka ƙunshi masu gabatar da ƙara na cikin gida waɗanda aka ba su goyon bayan kuɗi da gudanarwa daga abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa don hanzarta aiwatar da mahimman ƙararraki da hukunta manyan laifuka. A karkashin kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2653, gwamnatin Haiti ta kuma yi aiki tare da ma’aikatan kasashen waje, musamman Amurka da Kanada, don sanya takunkumin kan manyan gungun ƴan daban siyasa da ake fako.
Shawo Kan Rashin Hukunta Laifuka don Yaƙar Black Axe
Bisa la’akari da katsalandan da ƴan siyasa ke yi da ke takaita gurfanar da laifukan Black Axe a Najeriya, gwamnatin tarayya da na jihohi za su bukaci kara yawan dokokin da suke da su don kare bangaren shari’a daga cin zarafi. Wannan na iya nufin kafa sashin shari’a mai cin gashin kansa don gurfanar da manyan masu fada a ji na Black Axe da abokansu na siyasa. Najeriya za ta kuma iya yin la’akari da yin aiki tare da abokan huldar kasa da kasa don kakaba takunkumi kan wasu jama’a da aka san su a matsayin masu goyon bayan Black Axe don rage karfin siyasa da waɗannan mutane ke amfani da su, kamar yadda aka yi ga fitattun masu daukar nauyin kungiyoyin a Haiti.
Yaki da Black Axe zai kuma haifar da wani babban gangamin wayar da kan jama’a wanda zai sanya shugabannin al’umma, addini, gargajiya, da na ilimi don wayar da kan jama’a game da barazanar kungiyoyin masu aikata laifuka na asiri da kuma hana matasa shiga.
Ana buƙatar bincike kan gwamnatoci a ƙasar China da Hadaddiyar Daular Larabawa waɗanda ke zama manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗi don haramtaccen cinikin Black Axe.
A matakin kasa da kasa, ayyukan INTERPOL na kasashe da yawa sun kawo cikas ga ayyukan Black Axe kuma za su kasance masu mahimmanci. INTERPOL na iya shawarar faɗaɗa ayyukan ƴan sanda na kasa da kasa ta hanyar ƙarin ƙasashen Afirka ganin cewa Black Axe na ci gaba da kasancewa a cikin ƙasashen Afirka da dama waɗanda ba sa cikin ayyukanta na baya.
Har ila yau, ƴan sana’o’i a Afirka da ketare za su iya ƙara ƙokari don wayar da kan ma’aikatansu game da zamba na BEC. Hakanan kamfanoni za su iya yanke shawarar amfani da sofwayan kwamfuta wanda ke gane saƙon imel masu mummunan nufi da amfani da ƙirkirarriyar basira don ba wa jami’an tsaro damar tattara bayanai kan ayyukansu.
A ƙarshe ana buƙatar bincike kan gwamnatocin ƙasashen China da Hadaddiyar Daular Larabawa waɗanda ke zama manyan cibiyoyin hada-hadar kuɗin haramtaccen cinikin Black Axe. Sa ido mai tsauri kan kasafin kuɗi a cikin waɗannan cibiyoyin kuɗi na iya yin tasiri sosai ga tafiyar da harkokin kuɗi na Black Axe, ya toshe hanyoyin samun kuɗin shiga da ƙarfin aiki.
Dakta Matthew La Lime Mai Bincike ne tare da Cibiyar Nazarin Dabarun Afirka.
Ƙarin bayanai
- Goeff White, Rinsed: Daga Katel zuwa Crypto: Yadda Masana’antar Fasaha ke Wanke Kuɗi wa Mafi Munanan Masu Aikata Laifukan Duniya (London: Penguin Books, 2024).
- Suleman Lazarus, “Cibiyoyin Masu Aikata Laifukan Yanar Gizo da Tsarin Aikin Masu Zamban Imel na Kasuwanci (BEC): Fahimta daga Halayyar Saɓani na Ƙungiyan ‘Black Axe’” (2024), 1-25.
- Charlie Northcott, “Yan sandan Duniya a tseren Makamai na Fasaha tare da Mafiyan Najeriya” BBC, 27 ga Agusta, 2024.
- “Black Axe: Ƙungiyan Asirin Mafiya na Najeriya,” BBC Africa Eye Documentary, BBC, 10 ga Disamba, 2022.
- Nate Allen, Matthew La Lime, da Tomslin Samme-Nlar, “Munanan Ɓangarori da Intanet ke Ƙunsa: Fuskantar Barazana ta Intanet da ke Afirka” Ƙungiyar Yaki da Manyan Laifukan Kasa da Kasa, Disamban 2022.
- Corentin Cohen, “Ƙungiyoyin Najeriya Sun Fito Su Ci Nasarar Duniya?” Les études du CERI N˚ 258 bis, SciencesPo, Disamban 2021.
- Sean Williams, “Black Axe: Yadda Ƙungiyar Ƴancin Afirka ta Ɓata hanya” Mujallar Harper, Satumban 2019.
- Stephen Ellis, Duhu na Yanzu: Tarihin Manyan Laifukan Najeriya (Oxford: Oxford University Press, 2016).